Jamiyar APC Zata Kai Gwamnatin Jihar Bauchi Kotu

APC

Jamiyar APC ta jihar Bauchi ta sha alwashin gurfanar da gwamnatin jihar Bauchi a kotu

Jamiyar APC ta jihar Bauchi ta sha alwashin gurfanar da gwamnatin jihar Bauchi ta PDP a kotu, domin ta kalubalanci hukuncin da Gwamna jihar Bauchi Mallam Isa Yuguda ya dauka na sake nada wasu sabobin shuwagabanin kanana hukumomi, a jihar Bauchi.

Batun zaben kananan hukumomi a jihar Bauchi abu ne dake ciwa yawancin ‘yan jihar tuwo a kwarya, masammam ma ‘yan siyasa.

Gwamnatin jihar Bauchi, da tayi zama da ‘yan siyasar jihar dangane da batun shirya zaben kananan hukumomi a wannan shekara amma daga baya sai ta noke.

Kakakin ‘yan takaran kananan hukumomi na jamiyar APC na jihar Bauchi yace nada kantomomi abun bakin ciki ne, ya kara da cewa wannan na nuni cewa maganan zabe babu kennan.

Alhaji Kabiru Muhammad, mai tallafawa Gwamna jihar Bauchi a fanin siyasa yace Gwamnati, bata nayin abun da ta keso bane bukatun jama’a take aiwatarwa.

Your browser doesn’t support HTML5

APC zata kai gwamnatin jihar bauchi kotu - 3'15"