Jose Mourinho Yace Allah Ya Raka Taki Gona...

José Mourinho

Jose Mourinho yace Allah ya raka taki gona, a lokacin da yake magana game dan wasan baya na Chelsea David Luiz, wanda a watan da ya shige ya koma kungiyar PSG ta Paris a kan tsabar kudi Euro miliyan 50.

David Luiz ya fuskanci suka a saboda bai burge yadda aka zata lokacin gasar cin kofin kwallon duniya ba.

A yanzu Mourinho yace a zahiri, kungiyar Chelsea ta fi karfi ma a bayan da shi Luiz ya bar ta, bayan ya shafe shekaru 3 a can.

Mourinho yace ai a kakar kwallon da ta shige ma, ba shine dan wasan farko da yake zaba a tsakanin masu tsaron baya ba. John Terry da Gary Cahill sune zabinsa a ‘yan baya. Yace babu shakka a tsakiya, Luiz ya tabuka wani abu, musamman a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai a lokacin da Nemanja Matic ya kasa iya wasa. Amma a bana, Matic zai buga mana a gasar ta Turai, don haka, babu abinda zamu rasa.

Yace a lallai, Luiz ya taka rawa sosai a kulob din Chelsea, kuma mutumin kwarai ne. Amma a fagen kwallo, babu abinda zasu yi hasara da komawarsa PSG. A bana kungiyarmu ta fi ta bara karfi, in ji shi.