Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arsene Wenger Yace Firimiya Lig ta Bana Ta Arsenal Ce


'Yan wasan Arsenal sun dauki manajansu, Arsene Wenger, bayan da suka doke Hull City suka lashe kofin Kalubalenka, FA Cup, na Ingila ranar asabar 17 Mayu 2014
'Yan wasan Arsenal sun dauki manajansu, Arsene Wenger, bayan da suka doke Hull City suka lashe kofin Kalubalenka, FA Cup, na Ingila ranar asabar 17 Mayu 2014

Arsene Wenger, yace a bana kam, yayi imani kuma yana da kwarin guiwar cewa kungiyarsa ta Arsenal tana da ‘yan wasa da kwarewar da zata iya lashe gasar lig-lig ta Firimiya ta kasar Ingila.

Rabon da Arsenal ta lashe wani kofi tun shekaru 9 da suka shige, im ban da kofin kalubalenka da ta lashe a watan Mayu bayan da ta doke kungiyar Hull City.

A shekarar kwallo da ta shige, Arsenal ta yi kamar zata lashe gasar Firimiya Lig, amma daga baya sai ta fara yin tuntube, kuma aka kammala kakar kwallo tana matsayi na 4.

Wenger, ya nuna aniyarsa a bana din ta hanyar sayo dan wasa Alexis Sanchez daga kungiyar FC Barcelona a kan Euro miliyan 40. Bayan nan ya kara ‘yan wasanni irinsu Calum Chambers, Mathieu Debuchy da kuma David Ospina.

Arsene Wenger, wanda shi kansa ya rattaba hannu kan sabon kwantarakin shekaru 3 da Arsenal a watan Mayu, yace a bana kam, ya samu kwarin guiwa fiye da yadda abubuwa suke ma kulob din a farkon shekarar kwallon da ta shige.

Yace a bara din ma, maki 7 kawai ya raba tsakaninsu da Manchester City wadda ta zamo zakarar Firimiya Lig ta Ingila.

XS
SM
MD
LG