Ikirarin Fintiri Da Magoya Bayansa Yaudara Ce Kawai In Ji Ahmed Gulak

Ahmed Gulak

Dambarwa ta kaure a Adamawa a bayan da mai rikon mukamin gwamnan Jihar, Umaru Fintiri, yace shi ma zai shiga takarar neman kujerar a inuwar jam’iyyar PDP.

Wani jigon jam'iyyar PDP a Adamawa, Alhaji Abubakar Abdullahi Sardaunan Michika, yace babu laifi ga mukaddashin gwamnan ya nemi takarar wannan kujera da aka ba shi riko domin jama'a ne suka bukace shi da yayi hakan. A cewarsa, mutane sun ga alamar haske ne shi yasa suka bukaci8 ya nemi kujerar.

Amma tsohon mai ba shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Ahmad Gulak, wanda shi ma ke kwadayin hawa kan wannan kujerar, yace zancen Fintiri da na magoya bayansa yaudara ce kawai.

"Kowa zai ce maka jama'a, wasu jama'a ne suke wannan magana" in ji Gulak? Yace yana bayarda shawara ga mukaddashin gwamnan da ya rike wannan mukami na watanni ukun da tsarin mulki ya ba shi, sannan ya bar masu neman tsayawa su tsaya.

Gulak ya kara da cewa in kuma bai ji shawarar ba, to, "duk wanda ya kona rumbunsa, ya san inda toka ke da tsada ne."

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, Alhaji Ahmed Lawal, yace maitar mukaddashin gwamnan ce take kara fitowa a saboda a lokacin da ya dauko batun tsige gwamna Murtala Nyako a gaban majalisa, da yawa cikin manyan PDP sun dauka yana sonsu ne, amma a cewarsa, yanzu 'yar manuniya ta nuna.

Your browser doesn’t support HTML5

Ikirarin Fintiri Da Na Magoya Bayansa Yaudara Ce Kawai In Ji Gulak - 1'22"

ACT 1

TEXT: Sai dai wasu ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP masu kwadayin wannan kujera, irinsu tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Ahmed Gulak, sun ce ikirarin Fintiri da magoya bayansa yaudara ce kawai

ACT: Gulak

TEXT: Su ma ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta APC a Jihar Adamawa sun ce da ma sun fada…

TEXT: APC