Mohammed Ibn Chambas Ya Zamo Shugaban Ofishin MDD A Afirka Ta Yamma

Mohammed Ibn Chambas

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ya bada sanartwar nada Mohammed Ibn Chambas dan kasar Ghana a zaman Wakili na Musamman, kuma shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Afirka ta Yamma (UNOWA).

Ibn Chambas zai maye gurbin Saide Djinnit dan kasar Aljeriya, wanda babban sakataren ya bayyana godiya da irin jagtorancin da yayi a ofishin majalisar na Afirka ta Yamma.

Mohammed Ibn Chambas ya kware sosai a fannin ayyukan diflomasiyya da na gwamnati na kasa da kasa. Tun watan Disamba na 2012 yake rike da mukamin Wakili na Musamman na Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya a Darfur.

Daga 2010 zuwa 2012, Ibn Chambas shi ne babban sakataren kungiyar kasashen Afirka, carribean da Pacific.

Kafin nan ya rike mukamin shugaban kungiyar ECOWAS daga 2006 zuwa 2009, kuma yayi babban sakatarenta daga 2002 zuwa 2005.

Yayi dan majalisar dokokin kasar Ghana, kuma ya rike mukaman mukaddashin ministan harkokin waje da irin wannan mukami a ma'aikatar ilmi.