Hukumomin 'yan sanda a Kano, cibiyar kasuwanci ta yankin arewacin Najeriya, sun ce mutane akalla 6 suka mutu a lokacin da wani bam da aka dana cikin wata mota ya tashi a wani gidan mai dake unguwar Hotoro, a kan hanyar zuwa Maiduguri da Bauchi.
Wakilin Muryar AMurka, Mahmud Ibrahim Kwari, ya ce wannan bam da ya tashi da misalin karfe 7:30 na maraicen yau jumma'a, an dana shi ne cikin wata mota kirar Toyota Sienna, wadda ta tashi a wani gidan mai Nagarsuku Filling Station, wanda ke daura da gidan man NNPC Mega Station, inda kwanakin baya aka samu tashin wani bam din.
Wakilin namu yace akwai wuraren binciken ababen hawa na sojoji da 'yan sanda har guda biyu dake dab da wannan gidan mai da kuma mahadar, kuma akwai yiwuwar cewa an auna wannan harin en a kan jami'an tsaron da aka san su na ajiye motocinsu a nan a lokacin da suke gudanar da aikii a nan kusa.
Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan Jihar Kano, ASP Magaji Musa Majiya, ya fadawa Mahmud Kwari cewa daga cikin mutane 6 da suka mutu akwai dan sanda guda daya.
Shi ma maharin ya mutu a lokacin da bam din ya tashi cikin motarsa.
Sauran mutane 5 da suka mutu fararen hula ne.
Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin ya zuwa yanzu, amma an fi kyautata zaton cewa 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram wadanda sun sha kai hare-hare a birnin na Kano a can baya.