WASHINGTON, DC —
Dandalin VOA ya zanta da wata mace kuma injiniyace wacce ta taka muhimmiyar rawa, wajen zana taswirar gidaje ga ‘yan uwanta mata.
Injiniya Maryam Bello ta bayyana mana yadda take gudanar da wannan sana’a tata inda tace, ta karanci Injiniyarin a makaranta wato bangaren zane zane, kuma yanzu haka shine sana’ar ta domin tana zana gidaje, gada, dakuma hanyoyi da kwalbati da dai sauransu.
Tace abinda ya shawo kanta wajen sha’awa ta wannan sana’a, shine yadai fara saboda tana son lissafi, kuma aikin injiniya na bukatar lissafi taga kuma ya dace tunda tana da sha’awar lissafi. Saurari hirar da Baraka Bashir da Maryam