Ba Za A Tuhumi Dan Sanda Bature Da Ya Kashe Bakar Fata Ba

Karshenta dai ayarin masu bincike kan ko an aikata laifi ko a'a sun yanke shawarar cewa babu wata hujja ta tuhumar dan sanda Darren Wilson dangane da harbewa da kashe wani saurayi bakar fata mai suna Michael Brown, wanda ba ya dauke da wani makami a Jihar Missouri.

Wannan kisa ya kara haddasa zaman doya da manja a tsakanin mutanen garin Ferguson dake bayan garin birnin St. Louis, wanda kuma mafi yawan al'ummarsa bakar fata ne, da rundunar 'yan sandan wannan gari wadanda yawancinsu turawa ne.

Tarzoma ta barke kwana guda bayan kisan, kuma an shafe makonni ana dauki ba dadi a tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga.

Yanzu dai babban abinda ake fargaba shi ne abinda zai biyo bayan wannan shawara. An kafa dokar ta baci a jihar, an kuma soke hutun dukkan 'yan sandan wannan gari tare da girka dogarawan tsaron cikin gida domin su taimakawa 'yan sanda wajen kwantar da wutar duk wata tarzomar da zata iya tashi.