Ana zaman zullumi a yayin da ake jiran a ji ko gungun masu bincike a Jihar Missouri dake nan Amurka sun yarda a gurfanar da wani dan sanda bature mai suna Darren Wilson a gaban kotu ko kuma a'a, dangane da harbe wani saurayi bakar fata mai suna Michael Brown wanda ba ya dauke da makami.
Gwamna Jay Nixon na jihar Missouri yayi kiran da a kwantar da hankula, da kai zuciya nesa yayin da ake jiran jin ta bakin masu binciken. Nixon yace an girka dogarawan tsaron cikin gida domin bayar da tallafi ga 'yan sanda wajen kwantar da wutar duk wata fitinar da ka iya tashi.
Ana sa ran 'yan zanga-zanga daga kowace kusurwa ta Amurka zasu hallara a Ferguson idan har masu binciken suka ce dan sandan bai aikata wani laifi ba.
A ranar 9 ga watan Agusta Darren Wilson ya bindige ya kashe Michael Brown a tsakiyar titi a garin Ferguson dake bayan garin birnin St. Louis, a wani lamarin da ake cacar baki a kan yadda ya wakana.
Wannan kisan ya haddasa mummunar zanga-zangar makonni tare da kwasar ganima.