An Kashe Hafsan Sojan Da Aka Sace A Kaduna

Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya ta bayarda sanarwar cewa an kashe wani hafsan sojan kasar da aka sace shekaranjiya lahadi a garin kaduna.

Wata sanarwar da mai rikon mukamin darektan yada labarai na rundunar sojojin kasa, Kanar Sani Kukasheka Usman, ya bayar, ta ce yau talata da misalin karfe 6 na maraice aka tsinci gawar Kanar Ismaila Yunusa a dab da kauyen Ajyaita a babbar hanyar Byepass ta gabas ta Kaduna.

Sanarwar ta ce da alamun tun ranar da aka sace Kanar Yunusa aka kashe shi, domin har gawarsa ta fara rubewa a lokacin da aka same ta.

Sanarwar ta lashi takobin farauto wadanda suka aikata wannan abu tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukumcin da ya dace.