Majalisar Wakilan Amurka Ta Amince Da Wani Tanajin Doka

An amince da dokar da kuri'u 223 akasin 195, ya maye gurbin kudurin dokar makon jiya, wanda ya jefa Majalisar cikin rudu.

Majalisar Wakilan Amurka ta amince da wani tanajin doka, wanda ya haramta nuna wariyar jinsi wajen bayar da kwantaragin gwamnati.

Tanajin dokar, wanda aka amince da shi jiya Laraba da kuri'u 223 akasin 195, ya maye gurbin kudurin dokar makon jiya, wanda ya jefa Majalisar mai rinjayen 'yan Republican cikin rudu. Ana gab da amincewa da kudurin dokar yayin wata gyara ga kudurin dokar kashe-kashen kudin soji, sai wasu daga cikin 'yan Majalisan 'yan Republican, wadanda da farko su ka amince da wancan kudirin dokar, su ka canza ra'ayi saboda matsin lamba daga shugabannin jam'iyyarsu, don haka aka sake gabatar da shi inda aka soke shi da kuri'a guda.

Wancan sauyin ya janyo korafi sosai daga 'yan jam'iyyar Democrat da ke Majalisar, wadanda su ka zargi 'yan Republican da goyon bayan wariyar da ake nuna ma 'yan luwadi da madugo da masu jinsi biyu da wadanda su ka canza jinsinsu.

Dan jam'iyyar Democrat daga New York Sean Patrick Maloney, wanda ya fara gabatar da kudurin dokar, wanda shi kansa dan luwadi ne, ya sake gabatar da kudurin dokar yayin wata gyara ga kudurin kashi kudin Ma'aikatar Makamashi.