Majalisar Dattawan Brazil Ta Fara Yunkurin Tsige Shugabar Kasar

Shugabar Brazil Dilma Rousseff da majalisar dattawan kasar ke kokarin tsigeta daga mukaminta

Majalisar dattijan Brazil ta fara kada kuri’a akan tsige shugaba Dalima Roussef, yunkuri da zai kai ga mika ragamar mulki ga mataimakinta Michel Temer a hukumance wanda a halin yanzu yakwe rikon kwarya


Mahawarar majalisar dattijan ta dauki lokaci har izuwa safiyar yau Laraba kuma sakamakon kuri’ar ya bayyana karara mutane 59 masu neman a tsigeta sun fi rinjayi akan mutane 21 masu ra’ayinta. Majalisar tana bukatar karamin rinjaye ne kafin a gurfanar da ita gaban kotu, amma bayan shari’ar majalisar zata bukaci kashi biyu cikin ukku a karshen watan Agusta.


Tun a cikin watan Mayu ne Majalisar Dattijan ta dakatar da ita bisa tuhumar da ake mata na yaudara akan wasu alkalumma da ta bayar akan kasafin kudi don nuna wa jama’a tattalin arzikin kasar na tafiya yanda yakamata don a sake zabanta a shekarar 2014. A cikin shirye shiryen gabatar da ita gaban doka shugaba Roussef tana kan bakanta cewa bata aikata laifi ba.