Iyaye a Kano sun koka game da yawaitar satar yaran su kanana

Wasu Yaran Da aka Sace a Kano

Iyaye a Kano sun koka game da yawaitar ayyukan bata gari na satar yaran su kanana a wasu sassan birnin, lamarin da sukace na barazana ga makomar iyalai da al'uma baki daya.

Daga watan Janairun bana zuwa yanzu kididdiga ta nuna cewa an sace yara kanana yan kasa da shekaru 5 kimamin tamanin daga wasu unguwanin birnin Kanon Dabo.

Wasu iyaye sun yiwa wakilan sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari bayanin yadda aka aka sace 'ya'yansu.

Wata mace ta baiyana yadda kimamin watani goma sha daya da suka shige aka sace mata da. Tace ta kai kukanta har wurin gwamnan jihar Kano wanda yayi alkawarin cewa gwamnatinsa zata taimaka. Amma har yanzu shiru kake ji babu abinda aka yi

Ita ma Mallama Medina Ahmed wadda ke zaune a anguwar Hotoro tace yaront a dan shekara biyu aka sace. Tace wani yaro ne ya shiga har cikin gidanta kamar wanda yaje yin bara, Daga baran, tace suka nemi danta sama da kasa, amma basu gansi ba.

A saboda haka suke neman agajin gwamnan jihar Kano da ya yiwa Allah ya shigo wanan al'amari ya agaza musu.

Anyi zargin cewa wasu bata gari ne suka amda da yara yan shekaru 10 zuwa 12 wajen aikata wannan ta'ada.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda ake sace yara a Kano 3"09