Tagawar Afghanistan Kan Zaman Lafiya Ta Isa Pakistan

Tawagar Afghanistan da Wakilan Pakistan

Tawagar Afghanistan ta isa Pakistan domin tattaunawa akan yadda kasashen zasu cimma zaman lafiya da sulhuntawa a kasar ta Afghanistan

Wata tawaga akan matakan tsaro mai karfin gaske ta kasar Afghanistan ta kai ziyara zuwa kasar Pakistan a jiya Talata domin tattaunawa ta musammam da jami’an gwamnatin na Pakistan akan yadda kasashen biyu zasu gudanar da samun zaman lafiya da sulhuntawa a kasar ta Afghanistan.

Wasu majiya masu tushe daga kasar ta Afghanistan sun shaidawa Muryar Amurka cewa tawagar ta Atmar ta kasance a Islamabad har na tsawon wasu sao’i domin ta gana da shugaban hukumar tattara bayanan sirrri na kasar , dama babban jami’in kula da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro na kasar.

Suka ce tattaunawar da jami’an suka yi ta mayar da hankali akan rikicin gwamnatin kasar ta Afghanistan da ‘yan kungiyarTaliban ne, da kuma dakatar da bude wuta har na tsawon kwanaki ukkun da musulmi suka yi suna bikin karamar sallah.

Sai dai kungiyar ta Talibn taki ta kara adaddin kwanakin da ta diba na dakatar da bude wuta wanda ya kawo karshe a ranar Lahadi, wanda kuma tuni kungiyar ta koma bakin daga.

Sai dai gwamnatin ta Afghanistan ta dauka cewa za a kawo karshen bude wuta a ranar Laraba wato yau ke nan.