Ana Cigaba Da Neman Yaran Da Suka Makale A Kogon Tham Luang A Thailand

Yau kwana na 4 kenan da ake cigaba da neman matasa yan wasan kwallon kafa su 12 da mai horaswar su, waddanda ake da tabbacin cewa sun makale a cikin wani Kogo da yayi ambaliya a kasar Thailand.

Yayinda tawagar kwararrun sojojin ruwa suka kara shiga kogon Tham Luang a arewacin lardin Chaing Rai, Iyayen yaran sun taru a wajen kogon suna adu'ar Allah ya maido musu su lafiya.

Ranar Asabar da ta gabata ne aka bayana batar yaran da mai horaswar su, bayan basu dawo daga horar wassan kwallon kafa ba. an fara cigiyar ne bayan an gano kekunan yaran a wajen

kogon. Jami'ain haddadun kogon na zargin cewa waddanda ake cigiya na mafaka cahn cikin wani daki dake cikin kogon.Baya ga sojojin ruwa dake cigiyar su, ana amfanin da wasu na'urorin karkashin ruwa don gano su.

Kogon na yawan ambaliya yayinda da damina ya kankama, wanda ke farawa daga watan Yuni har izuwa watan Octoba.