Kungiyar Washington Redskins

  • Murtala Sanyinna

Washington Redskins

Kungiyar kwallon zari-ka-ruga ta Washington Redskins ta tabbatar da sauya sunanta, sakamakon matsin lambar da ta ke fuskantar daga masu daukar nauyinta, dangane da sunan na ta da ake ganin yana da alaka da wariyar launin fata.

Tun a farkon wannan watan ne kungiyar ta sanar da cewa ta soma nazarin yin sauyi a sunan na ta, a daidai lokacin da ake ta yin zanga-zangar kin jinin wariyar launin fata a Amurka, biyo bayan mutuwar George Floyd a ranar 25 ga watan Mayu a birnin Minneapolis.

Kungiyar ta ce ta sauya suna da kuma tambarin kungiyar baki daya, duk da ya ke har yanzu ana nan ana nazarin sabon sunan da za’a sanya mata.

'yan wasan Washington Redskins


Mamallakin kungiyar Dan Snyder, ya dauki tsawon lokaci yana yin watsi da kiraye-kirayen sauya mata suna, to amma daga baya ya sake tunani sakamakon karuwar matsin lamba da barkewar zanga-zangar a Amurka.

Hatta Bankin Amurka da ke daukar nauyin kungiyar, ya ce ya “karfafa mata gwiwar sauya sunan.” Shugaban Amurka Donald Trump ya soki lamirin matakin kungiyar na sauya sunanta.

An kirkiro kungiyar ne a shekara ta 1932 da sunan Boston Braves, inda daga bisani a shekarar 1933, aka ba ta sunan na ta na yanzu, kafin ta dawo Washington DC bayan shekaru 4.