DOMIN IYALI: Matan Najeriya Da Zaben 2023-Kashi Na Biyu, Yuli, 07, 2022

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye da mu, makon jiya muka fara nazari kan kalubalen da ke gaban mata a cimma burinsu na samun kaso 35 cikin dari na guraban siyasa a Najeriya a daidai lokacin da gangar siyasa take amo a kasar na shirin babban zabe farkon shekara badi.

Yau ma, muna tare da bakin da muka gayyata domin nazarin lamarin da neman mafita Madam Eneh Ede ‘yar fafatukar kare hakkokin mata, kuma wadda ta tsaya takara a matsayin mataimakiyar gwamna a jihar Binuwe a zaben da jam’iyarta ta sha kaye, da ‘yar gwaggwarmaya Barrister Hassana Ayuba Mairiga,, da kuma dan siyasa a jihar Kano Nasir Shuaibu Marmara.

Jagorar tattaunawar Medina Dauda, ta tambayi Barrista Hassana ko da gaske ne bayanin da Nasir Shu’aibu ya yi cewa, mata suna riga-malam Masallaci a neman mukaman siyasa ba tare da tsayawa su kware ba.

Saurari shirin domin jin amsar wannan tambaya da kuma wadansu bayanai.

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Matan Najeriya Da Zaben 2023-Kashi Na Biyu-10:00"