Kotu Ta Amince A Ci Gaba Da Shari'ar Trump A Ranar 25 Ga Watan Maris

AP EXPLICA-ELECCIONES 2024-TRUMP

Alkali Juan Manuel a wata kotun birnin, ya ce shari’ar da ake tuhumar tsohon Shugaban Amurka Donald Trump da laifin biyan kudin toshiyar baki za ta ci gaba da wakana kamar yadda aka tsara, inda za a zabi masu taya alkali yanke hukunci daga ranar 25 ga watan Maris kamar yadda aka shirya tun farko.

A kwanannan Trump ya nemi a dage sauraren karar sai bayan an kammala zaben bana, wanda za a yi a watan Nuwamba.

Trump ya isa kotun da misalin karfe tara na safe a ranar Alhamis, wannan kuma shi ne karon farko da ya koma birnin na New York kan wannan shari’a, wacce ta zamanto ta farko a tarihin Amurka da ake tuhumar wani tsohon shugaban kasa da aikata laifi.

Zaman kotun ya wakana ne a kotun da Trump ya amsa cewa ba shi da laifi a tuhumar da aka masa a watan Afrilun da ya gabata, inda aka zarge shi da laifin saka bayanan karya a harkokin kasuwancinsa.

Masu shigar da kara na tuhumar kamfanin Trump, wanda dan Republican ne, da laifin ba da bayanan bogi da nufin yin rufa-rufa kan batun wata mu’amulla ta badala da ake zargin ya yi da wata mata kafin ya zama shugaban kasa.

Shi dai Trump ya musanta aikata ba daidai ba yayin da lauyoyinsa ke cewa shari’ar bita-da-kullin siyasa ce.