Jirgin Saman Fasinja Ya Fadi A Kasar Azerbaijan

Wani jirgin saman fasinja na kasar Azerbaijan dake dauke da mutane 23 ya fadi a bayan garin Baku, babban birnin kasar. Jami’ai suka ce sun yi imanin babu mutum guda da ya kubuta da rai a cikin jirgin.

Hukumomin Azerbaijan sun ce jirgin ya bace daga na’urar hango jirage jim kadan a bayan tashinsa daga birnin Baku jiya jumma’a. Akwai fasinjoji 18 da ma’aikata 5 a cikin jirgin.

Wannan jirgi kirar Antonov An-140 mai farfela biyu, ya doshi birnin Aktau ne dake kasar Kazakhstan a tsallaken tekun Caspian. Har yanzu babu bayani na musabbabin faduwar wannan jirgin sama.

A wani labarin dabam kuma, wani karamin jirgin sama na soja ya fadi a wani yanki mai tsaunuka na arewa maso yammacin Colombia, ya kashe sojoji biyu da fararen hula biyu a ciki.

Hukumomi a Bogota sun ce wannan jirgin sama kirar Cessna ya fadi jiya jumma’a a kusa da garin Jardin dake lardin Antioquia. Suka ce mutum na biyar dake cikin jirgin, wani soja, ya ji rauni.

Jami’an kula da zirga zirgar jiragen saman fararen hula na kasar ta Colombia ba su bayar da karin bayani na aikin da mutanen keyi ko inda suka dosa ko kuma musabbabin wannan hatsari ba.