Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Mutane 153 Dake Cikin Jirgin Dana Air Sun Mutu


Jirgin ya ci karo da wani gini mai hawa biyu, ya haddasa barkewar wuta a wata unguwar dake cike da mutane a Lagos, yayin da yake kokarin sauka daga Abuja.

Jami'an Najeriya sun ce dukkan mutane dari da hamsin da uku (153) dake cikin wani jirgin saman safarar fasinja sun mutu a lokacin da jirgin ya fado kan wani gini a Lagos.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a kasar domin tunawa da mamatan, ya kuma bayar da umurnin a gudanar da bincike sosai kan wannan bala'in.

Jami'an Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Saman farar hula ta Najeriya sun ce wannan jirgi ya taso ne lahadi daga Abuja a kan hanyar zuwa Lagos, sai ya ci karo da wani gini mai hawa biyu a wata unguwar dake cike sosai da jama'a a Lagos, ya sa gine-ginen dake wurin suka kama da wuta.

Ba a san ko akwai wasu mutanen a kasa wadanda suka mutu a sanadin fadowar jirgin ba.

Kamfanin safarar jiragen saman Dana Airlines kamfani ne mai gudanar da harkar zirga-zirgar jiragen sama a cikin gida a Najeriya, kuma yana amfani da jirage samfurin Boeing MD-83 a tsakanin Abuja da Lagos, hanyar da tafiyar awa daya ce ta sama.

XS
SM
MD
LG