A BARI YA HUCE: Labarin Soja A Masallaci- Mayu, 22, 2021

Alheri Grace Abdu

A shirin wannan makon mun bada labarin da Muhammad malaminta mai dinki unguwar alheri Zuru ya aiko mana. Ga labarin nasa:

Zamu fara Sallah kenan liman ya waiwayo ya ce "Dan Allah jama'a a taimaka asa waya a silent," kowa ya yi shiru ya yi fuska. Sai wani Soja ya waigo fuska murtuke yace "duk wanda ana sallah wayar shi ta yi Ringing ni da shi," Nan take sai ga jama'a kowa ya sa hannu aljihu ya na zaro waya. Ni ma na zaro tawa duk da na san tana silent. amma dan in kara tabbatar wa, duk da haka ban gamsu ba na sa hannu na cire batirin na watsa su aljihu. Na kara sa hannu aljihu na zaro batirin na canja mai aljihu, tunani na idan suna aljihu daya za a iya samun akasi wayar ta kunnu sabod kayan bature ba tabbas.

Saurari cikakken shiri:

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce: Labarin Soja A Masallaci 24: 00"