Dubban mutane ne suka hallara a fadin India jiya Lahadi, suna bukatar ganin an yiwa 'yan mata biyu adalci sakamakon fyade da aka yi musu, lamari da ya sa 'yan kasar suke tamabayar me yasa kare 'yan mata da mata baki daya yake zama kalubale duk da dokoki masu tsanani da ake da su.
Wannan shine taron jama'a mafi girma da yake nuna fushinsu tun bayan fyade irin wadda ake kira giwa ta fadi da aka yiwa wata daliba a babban birnin kasar ta India, lamari da ya janyo zanga zanga a duk fadin kasar.
Dauke da kwalaye a biranen New Delhi, da Mumbai, da Bengaluru, da Kolkata, masu zanga zangar sun yi kiran da a dauki mataki cikin hanzari na hukunta wadanda suka aikata laifin, a kuma gaggauata shari'ar masu bata yara kanana tareda yanke musu hukunci mai tsanani. A rataya masu irin wannan laifin," kamar yadda wasu rubuce rubuce da suke kan kwalayen suke fadi.
Cikin masu zanga zangar harda wata ma'aikaciya 'yar shekaru 37 da haifuwa Aditi Sengupta. Tace ta kai intaha. Na gaji da yadda kasan nan take wulakanta mata.