A Indiya Wata Damisa Ta Haifi 'Ya'yanta A Cikin Bukkan Manoma

Your browser doesn’t support HTML5

Wata damisa ta zabi bukka daga wurin manomi inda ta haifi 'ya 'ya hudu a wani kauye da ke yankin Nashik na Yammacin Indiya, in ji jami'an gandun daji. Mazauna kauyen sun nuna damuwa game da sabbin baƙi kuma sun nemi a cire su, wani jami'i ya ce ba za a iya cire kananan yaran ba domin jarirai ne.