A Karon Farko An Fara Gwajin Allurar Rigakafin Coronavirus

Wani likita kenan yayin da yake gudanar da aikinsa.

Jami’an lafiya a Amurka sun ce a karon farko an fara gwajin allurar rigakafin cutar Coronavirus akan mutane, a cigaba da famar da masu ilimin kimiyya ke yi ta nemo maganin wannan babbar annoba.

Masana kimiyya na cibiyar bincike ta Kaiser Permanente da ke birnin Washington na jihar Seattle, sun fara bai wa wasu mutane masu koshin lafiya gwajin farko.

Hukumar Lafiya ta Amurka NIH, ta ce gwajin da ake ya hada da mutane masu koshin lafiya da shekarunsu ya fara daga 18 zuwa 55, wadanda za a baiwa allurar rigakafin zuwa watanni shida.

Masana kimiyya ne daga hukumar NIH da kamfanin Moderna, wanda ke birnin Cambride na jihar Massachuset suka kirkiro allurar rigakafin.