A Kasuwar Mogadishu Bam Ya Hallaka a Kalla Mutane 30

Fashewar Bam ya lalata shaguna masu yawa a wata kasuwa a Mogadishu.

A Somalia, jami'an kasar suka ce akalla mutane 30 ne suka halaka wsu da dama kuma suka jikkata lokacin da wani gagarumin bam da aka boye cikin wata mota ya tashi cikin wata kasuwa yayin da take cike da mutane a Mogadishu jiya Lahadi.

Fashewar ta tarwatse kasuwar wacce take da wani guri da ake kira kawo-Goday a gundumar da ake kira Wadajir.

Jami'an tsaro da kuma shaidun gani da ido suka ce bam din ya tashi ne yayin da mutane suke tafiyar da harkokin su. Sun ce wadanda harin ya rutsa da su sun hada da farar hula 'yan kasuwa da kuma sojojin gwamnati.

Babu wanda ya fito nan da nan ya dauki alhakin kai wannan hari, amma jami'ai suna zargin mayakan kungiyar al-shabab da kai harin.

Sabon shugaban kasar Mohammed Abdullah Farmajo yayi alwashin zai yi galaba kan kungiyar al-shabab a cikin sako da ya aike ta shafinsa na Twitter bayan da aka kai harin. Yayi Allah wadai da kakkausar lafazi, yace harin ya sake nuna "dabbanci da rashin imanin kungiyar".

Daga nan yayi kira ga 'yan kasar da dakarunta su hada kai domin nasara kan kungiyar.