A Nijar Ranar 28 ta Kowane Watan Satumba Ne Ranar Yaki da Safarar Mutane

Birji Rafini, Firayim Ministan Nijar

Tun shekarar 2015 bayan an gano gawarwaki 93 cikin hamada gwamnatin Nijar ta tsayar da kowace ranar 28 ta watan Satumba a matsayin ranar yaki da safarar mutane

Gano gawarwaki 93 a hamada da suka hada da yara 52 da mata 37 da maza hudu ya sa Jamhuriyar Nijar ta ayyana ranar 28 ta kowane watan Satumba a matsayin ranar yaki da safarar mutane.

Haka ma gwmnatin kasar ta kafa dokar da ta tsaurara yaki da safarar mutane. Ministan Shari'a Malam Maru Amadu ya bayyana irin kokarin da gwamnatin kasar ke yi domin yaki da masu safarar jama'a.

Yana mai cewa madu'un ranar ta bana shi ne kasafin dokar yaki da safarar jama'a saboda kada a raba safarar mutane da safarar bakin haure domin ceto wadanda ake cuta.

Bana jihar Agadez ce zata amshi bakuncin bikin. Wannan yakin da Nijar ta sa gabanta yana samun goyon bayan kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS ko CEDEAO.

Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Nijar Ranar 28 ta Kowace Watan Satumba Ce Ranar Yaki da Safarar Mutane -2' 21"