A Sakon Sallah, Gwamna da Shugabannin Jihar Neja Sun Kira A Yi Zaman Lafiya

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello

Shugabannin jama'a a jihar Neja sun yi anfani da bukukuwan sallah sun kira jama'arsu da su nemi zaman lafiya da juna saboda a samu cigaban kasa

Shugabannin sun janyo hankulan jama'a akan mahimmancin zaman lafiya tsakanin al'umma.

Bayan sakon alheri daga shugaban majalisar sarakunan jihar Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, shi ma gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello yayi fatan al'ummar jihar zasu gudanar da bukukuwan sallah a cikin kwanciyar hankali.

A jawabin da gwamnan ya yi yace "ina rokon al'ummar jihar Neja a yi wannan sallah cikin kwanciyar hankali saboda watan Ramadan wata ne na zaman lafiya", inji gwamnan.

Dangane da daukan matakan tsaro a lokacin bukukuwan sallah yace jami'an tsaro sun yi zama kuma sun kawo rahotonsu akan irin abubuwan da zasu yi su kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Su ma shugabannin Fulani sun ja hankalin matasansu tare da zuba 'yan sa kai da zasu dinga lura da take-taken matasansu domin kaucewa duk wani tashin hankali musamman lokacin bikin sallah. Malam Muhammad Shehu, daya daga cikin shugabannin yace sun yi kashedin a gujewa fadace-fadace domin sun sanya kwamandoji idan sun ga wadanda suke son yin fada su wargazasu

Dangane da matsalar ganin wata, shugaban kungiyar IZALA reshen jihar Shaikh Aliyu Adarawa ya bada shawara ga mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar.Yace a sha'anin ganin wata ba'a yanke lokaci a ce idan ba'a gani ba lokacin shi ke nan babu gaskiya. A Taraba an ce an ga wata. Yakamata Sarkin Musumi ya san kasar nada fadi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Sakon Sallah da Gwamna da Shugabannin Jihar Neja Sun Kira A Yi Zaman Lafiya - 2' 49"