Hattara: Wasu Miyagun Likitoci Suna Sacewa Da Fataucin Kodar Bil Adama

Ma’aikatar Lafiya a Najeriya ta ja hankalin masu tafiya jinya a kasashen waje da su yi hattara a saboda yadda ake samun rahotannin likitoci masu satar kodar jama'a, musamman a kasar Masar.

Ma’aikatar lafiyar tarayyar Najeriya ta fitarda wata sanarwa wadda ke jan hankalin ‘yan Najeriya akan suyi hattara a yayinda suke zuwa jinya a kasashen waje, musamman kasar Masar, ganin yadda wasu batagarin likitoci a kasar ke sace kodar mutanen da suka je jinya.

Dr. Rilwanu Mohammed, wani kwararren likita ne a Najeriya, ya fadi cewa Koda na da muhimmanci a cikin jikin dan’adam. Akwai lokutan da aka sami mutane sun je neman jinya amma an cire masu koda ba tare da saninsu ba a irin wadannan asibitocin dake kasashen waje. Sai in wata rashin lafiya ta taso likita ya bayyanawa mutum halin da yake ciki.

Ya kara da cewa ko a Najeriya ma akwai bukatar a ayi hattara. Dr. Rilwan ya kuma ce yana da matukar muhimmanci duk abinda za ayiwa mutum a asibiti a fahimtar da shi kuma a bashi rubutaccen bayani akan abinda za a yi masa.

Dr. Saleh Abba dake asibitin koyarwa na Aminu Kano, yace bai yi mamakin wannan batun ba, yadda likitocin kasar Masar ke sace kodar mutane. Ya ce ko a shekarar 2011, wata kungiya mai suna Coalition of Organ Failure Solution ta fitar wani rahoto dake nuna irin wadannan abubuwan dake faruwa.

Bayan kasar Masar, kasashe kamar India, da china da Columbia, da Philippines sun yi kaurin suna a fataucin koda, saboda kasashen ba su da wasu dokokin masu tsauri, A cewar Dr. Saleh.

Malam Kabiru Danladi Lawanti, ya fadi cewa neman kudi da rashin imani ne ke haddasa irin wadanna abubuwan. Ya kara da cewa ya kamata duk dan Najeriyar da zai fita waje neman magani/jinya, ya bi tsarin doka, ya kuma bi ta hanyar ma’aikatar harkokin waje. Bayan haka ofishin jakadancin Najeriya ya san abinda ake ciki, don a tabbatar da cewa asibitin yana da rijistar.

Your browser doesn’t support HTML5

Ayi hattara da miyagun likitoci masu fataucin kodar bil'adama - 3'00"