Abin Da Masu Kididdiga Ke Cewa Kan Sakamakon Farko

A lokacin da shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya gana Da Shugabanni Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

Masana a fannin kididdiga a Najeriya, sun fara tsokaci kan sakamakon zaben shugaban kasar da aka fara gabatarwa a hukumar zabe ta INEC da ke Abuja, babban birnin kasar.

A jiya Litinin aka fara tattarawa tare da sanar da sakamakon zabukan wasu jihohi, inda ya zuwa daren jiya jihohi 11 suka gabatar da sakamakonsu da kuma birnin Abuja.

“Yawanci kashi 25 ne kadai cikin wadannan jihohi suka jefa kuri’a, wasu kashi 27.” Inji Dr. Sadiq Umar masani a fannin kididdiga, wand aya koka da karancin masu fita kada kuri'a.

Daga cikin jihohin da suka gabatar da sakamakonsu, akwai Abia, Ekiti, Ebonyi da dai sauransu inda shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya ke gaba da kuri’u sama da dubu 400.

A jiya shugaban hukumar zaben ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya dage sauraren karbar sakamakon zuwa yau Talata inda za a fara da misalin karfe 10 na Safiya.

A lokacin dage zaman, Farfesa Yabuku ya yi fatan za a kammala gabatar da sakamakon daukacin jihohin a yau Talata, inda za a ci gaba da jihar Pilato.

Saurari cikakkiyar tattaunawar Nasiru Adamu El Hikaya da Dr. Sadiq Umar:

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Da Masu Kididdiga Ke Cewa Kan Sakamakon Farko - 24'8"