Abin Da Trump Ya Fada a Jawabin "Halin Da Kasa Ke Ciki"

Shugaba Donald Trump

Wannan ne karo na biyu da shugaba Donald Trump yayi Amurkawa jawabi na halin da kasar take ciki, inda ya tado batutuwa da dama, musamman batun bakin haure da kuma gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi amfani da jawabinsa na “Halin da kasa ke ciki”, wajen kara nuna muhimmancin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, da kuma sauran muhimman batutuwa.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a tsakanin gwamnatin kasar.

A daren jiya Talata shugaba Trump ya gabatar da jawabin nasa, Lokacin da aka yi wa shugaba Trump iso a zauren majalisa magoya bayan sa suka yi ta tafi.

Yayin jawabin nasa, shugaba Trump, ya yi kira ga manyan jam’iyyun kasar biyu cewa, Akwai bukatar ‘yan Republican da ‘yan Democrat, su sake hada karfi da karfe, domin tunkarar wannan matsala ta gaggawa da ta tunkare mu.

Majalisar Dokoki na da kwanaki goma ta amince da kudurin dokar da zai samar da kudaden tafiyar da gwamnati, domin mu kare kasarmu.

A lokacin da shugaba Trump ya ambaci cewa, akwai wani babban ayarin bakin haure da ke tunkarar Amurka, an ji wasu suna gunaguni.

Yayin da 'yan Democrat ke mayar da martani ga shugaban na Amuruka, Stacey Abrams, ta ce ta “raina yadda shugaba Trump ya zayyana matsalolin kasar, amma ta ce tana mai yi masa fatan ya samu nasara.

Abrams, wacce ta kusa lashe zaben gwamna da aka yi a watan Nuwamba a jihar Goergia ta yi kira da a sake lale wajen fito da muhimmancin yin adalci a fannin harkokin yau da kulluma musamman a fannin shari’a.