Abinci da Ake Ci Na da Nasaba da Bullar Sabbin Cututtuka - Masana

Dr Fatima Abubakar Atiku, Kwamishaniyar Kiwon Lafiya ta jihar Adamawa

A taron masana da aka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa dake Naijeria, an fadakar da jama’a kan alakar dake akwai tsakanin sabbin cututtuka dake addabar jama’a da irin abincin da ake ci da yadda aka sarafa abincin da yanayin inda aka da fashi

Yayin da a Najeriya ake samun bullar cututtuka daban daban a yan makwannin nan, kwararru kan lafiyar abinci na danganta lamarin da irin abincin da jama’a ke ci a yanzu.

A yan watannin nan akan samu bullar sabbin cututtukan da wasu ma ba’a sansu ba a baya, kamar yadda a yan makwannin nan aka samu bullar cutar kyandar biri da aka fi sani da Monkey Pox a turance.

To sai dai kuma yayin da likitoci ke kokarin shawo kan irin wadannan cututtuka, masu harkar cimaka na ganin akwai abun dubawa.

A wajen taron karawa juna sani da kwararru suka yi kan kiyaye lafiyar abinci a Yola, fadar jihar Adamawa, an karantar da jama’a muhimmanci kula da abincin da kuma matakan kariya daga sabbin cututtukan dake da alaka da abinci, musamman a wannan lokaci na hannu baka –hannu- kwarya.

Da yake jawabi a taron, wani kwararre kana shugaban tawagar, Pevora Chukwu, yayi bayanin hanyoyi da abubuwa goma da idan jama’a suka kiyaye su, zasu kubuta daga kamuwa daga cututtukar da ake dauka ta hanyar cin abinci.

Yace tsaftar shi kansa mai dafa abinci, da na muhallin dafa abincin duk suna daga cikin abubuwan dake tabbatar da ingancin abinci da lafiyar jama’a.

Sananniyar ‘yar jaridar nan ta Naijeriya, Moju Makanjuoela dake cikin tawagar, tace aikin kiyaye lafiyar abinci aiki ne na kowa da kowa kuma akwai abubuwa da dama da jama’a ke yi dake haifar da cututtuka ta hanyar abincin da suke ci.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Abinci da Ake Ci Nada Nasaba da Bullar Sabbin Cututtuka - Masana - 3' 59"