Adadin Masu Coronavirus a Najeriya Ya Zarta 7000

Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta NCDC ta fitar, sun nuna cewa akalla mutum 339 sun sake kamuwa da cutar COVID-19.

Ya zuwa yanzu dai adadin masu cutar gaba daya ya kai 7,016 a fadin kasar.

Har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba wajen masu kamuwa da cutar, inda aka samu karin mutum 139.

Bayan nan sai jihohin Kano da Oyo inda suka sami karin mutum 28, 11 a birnin tarayya Abuja, 25 a Edo, 22 a Katsina, 18 a Kaduna, 14 a Jigawa, 13 Yobe, 13 a Filato, 8 a Gombe, 5 a Ogun, 4 a Bauchi, 4 a Nasarawa, 3 a Delta, 2 a Ondo, sai kuma jihohin Adamawa da Rivers da suka samu daya-daya.

Mutum 211 kuma suka rasu sakamakon cutar yayin da mutum 1,907 suka warke.