Adadin Masu Cutar Coronavirus A Najeriya Ya Kai 2,802

Kusan mutane 100 ne suka mutu sakamakon cutar coronavirus a Najeriya, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya, NCDC.

Cibiyar ta tabbatar da sabbin kamuwa da cuter 245, Wanda ya ba da jumlar wadanda suka kamu da cutar a Najeriya 2,802.

Sabbin alkaluman sun hada da, Legos - 76, Katsiana - 37, Kano - 23, Jigawa - 32, Borno - 18, Bauchi - 9, Adamawa - 6, jihohin Oyo da Ogun na da biyar-biyar, sai jihohin Ekiti, Osun, Benue, Nijer da Zamfara na da guda daya-daya. Birnin tarayya Abuja na da 19.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 2,802 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 417 suka samu lafiya, sai mutane 83 da suka mutu.