Adadin Masu Kamuwa Da Cutar Coronavirus Ya Ragu A China

China ta bada rahoton cewa adadin masu kamuwa da sabuwar cutar Coronavirus wadda ta kashe sama da mutane 2,000 a fadin kasar ya ragu ainun, cutar dai ta fara ne sama da watannin biyu da suka gabata.

A jiya Laraba hukumar lafiyar China ta ce mutane 394 ne kacal aka tabbatar sun sake kamuwa da cutar ta Coronavirus samfurin COVID-19, idan aka kwatanta da mutane 1,749 da suka kamu da cutar a ranar Talata.

Wannan shine adadin raguwa mafi girma da aka gani tun daga watan da ya gabata. Adadin wadanda suka mutu kuma ya karu zuwa 2,118 bayan da wasu mutane 114 suka mutu sanadiyar kwayar cutar, yayin da gaba daya adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya karu zuwa 74,576.

A wajen China kuma, akalla mutane 11 aka sami rahoton sun mutu sanadiyar kwayar cutar, ciki har da mutum daya daga Koriya ta Kudu, sai kuma mutane biyu a Iran da kuma wasu miji da mata ‘yan kimanin shekaru 80 da haihuwa da suka shiga wani jirgin ruwan fasinja na Diamond Princess, wanda aka killace a tashar jiragen ruwan Yakohoma dake gabar tekun Japan tun lokacin da jirgin ya isa garin a ranar 3 ga watan Fabarairu.

Diamond Princess

Ana sa ran fasinjoji 600 za su bar jirgin a yau Alhamis, kwana daya bayan da fasinjoji 500 suka fita daga cikin sa, bayan da gwaje-gwajen jami’an kiwon lafiya suka nuna cewa basa dauke da cutar kuma basa nuna alamomin kamuwa da ita.