Adadin Wadanda Suka Kamu Da Cutar Kwalara Ya Karu A Mozambique

Jami’ai a yankin Mozambique da muguwar guguwa ta shafa sun ce adadin wadanda suka kamu da cutar kwalara ya karu daga mutane 5 a shekaranjiya Laraba zuwa mutane 139 a daren jiya Alhamis.

Kwalara wata cuta ce da ke bazuwa ta abinci ko ruwan shan dake dauke da kwayar cutar. Ta na haddasa gudawa da ammai akai akai dake tsotse ruwan jikin bil’adama, kuma a cikin ‘yan sa’o’i idan ba a nemi maganin ta ba ta kan iya kashe mutum.

Mummunan yanayin zama, kamar rashin tsabtataccen muhalli da kuma ruwan sha, a kasar biyo bayan mummunar guguwar da ta auku sune abubuwan da suka haddasa bazuwar cutar.

Hukumar lafiya ta duniya da ake kira WHO ta fada a farkon makon nan cewa zata aika allurar rigakafin cutar kwalara dubu 900 zuwa yankin.