Adadin Wadanda Suka Mutu a Harin Somalia Ya Karu

Ragowar wata mota da aka kai harin da ita a birnin Mogadishu na Somalia, a ranar 15 Yuni, 2019.

Shugaban kasar ta Somalia, Mohammed Abdullahi Farmajo, ya kwatanta harin a matsayin “tsananin mugunta da ragwanci” da ‘yan ta’addan suka nuna.

Hukumomi a Somalia sun ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin da aka kai a wani otel da ke kudancin birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa, ya haura zuwa 33.

Shugaban yankin Jubbaland, Ahmed Mohammed Islan, wanda aka fi sani da Madobe, ya ce an gano karin mutane 56 da suka ji raunuka a harin wanda aka kai a jiya Juma’a.

Ya kara da cewa, daga cikin wadanda suka mutu, har da ‘yan jarida biyu, da wani dan takarar shugaban kasa da za a yi na yankuna, da wani ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya, inda ya kara da cewa, daga cikin mamatan akwai, Amurkawa da ‘yan kasar Kenya da Birtaniya da Tanzania da kuma wani dan kasar Canada.

Jami’an tsaron yankin na Kismayo, sun fadawa Muryar Amurka cewa, sun kashe akalla maharan hudu daga cikin wadanda suka kai farmakin.

Wasu majiyoyi da Muryar Amurka ta tuntuba a asibiti, sun bayyana cewa an samu karin mutuwar fararen hula uku.

Shugaban kasar ta Somalia, Mohammed Abdullahi Farmajo, ya kwatanta harin a matsayin “tsananin mugunta da ragwanci” da ‘yan ta’addan suka nuna.