Kamar yadda alkalumma ke nunawa kawo yanzu akwai daruruwan yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu dake wasu sansanonin yan gudun hijira da aka tanadar.
To sai dai kuma kawo yanzu hukumomi a jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram yayiwa tu’annati na shirin rufe sansanonin dake jihar,batun da wasu yan gudun hijira ke ganin akwai abun dubawa.
Kamar wadannan yan gudun hijiran ,shima wani dan asalin yankin Michika ya bayyana abun da ya gani a yankunansu da yace ya kamata ayi karatun ta natsu.
To wai ko me ake ciki ne game da batun rufe sansanonin yan gudun hijiran? Sa’adu Bello dake zama jami’in hukumar dake kula da sansanonin yan gudun hijira a shiyar Adamawa da Taraba,wato NEMA, ya bayyana dalilan daukan wannan mataki.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5