Afghanistan Ta Tabbatar Da Mutuwar Mullah Mansoor

Mutane Tsaye a Gaban Motar Mullah Mansoor

Hukumar leken asiri ta Afghanistan, NDS, ta ba da tabbacin mutuwar shugaban kungiyar Taliban Mulla Akthar Mansoor.

Mullah ya rasu ne sanadiyar hare-haren sama da aka kai a yankin Pakistan da ke kusa da kan iyakar kasar ta Afghanistan.

Wata takaitacciyar sanarwa da hukumar ta NDS ta fitar a yau Lahadi a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa “Shugaban Taliban Mullah Akthar Mansoor ya mutu a harin sama da aka kai da misalin karfe 3:45 na yamma a yankin Dalbandin da ke Baluchistan.”

A yau Lahadi Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ke ziyara a kasar Myanmar, ya ce an kai harin ne kan Mansoor, saboda ya kasance barazana ga Amurka da fararen hulan Afghanistan da jami’an tsaronsu, kuma ya kasance yana adawa da shirin zaman lafiya da ake kokarin a cimma.