Afrika Ta Kudu: Adadin Masu Cutar Coronavirus Ya Karu

Karuwar mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Afrika ta Kudu ya sa shugaban kasar Cyril Ramaphosa sanar da tsauraran matakai don dakile yaduwar cutar. Cutar mai shafar numfashi ta zama annoba a duniya, wadda ta kama mutum fiye da 153,000 a fadin duniya, tun bayan bullar ta a kasar China a karshen shekarar 2019.

Tun bayan samun barkewar cutar karon farko a Afrika ta kudu ranar 5 ga watan Maris, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu har ya kai ga mutum 62, kuma hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana lamarin cutar a kasar a matsayin yuduwar cikin gida.

Shugaba Ramaphosa ya ce sun cimma matsaya akan daukar kwararan matakan gaggawa na dakile yaduwar cutar, don kare al’ummar kasar, kana da rage radadin cutar ga al’umma da kuma tattalin arziki.

Shugaba Ramaphosa ya yi wannan jawabin ne ta kafar talabijin jiya Lahadi da dare. Ya kara da cewa “mun ayyana daukar matakin gaggawa na kasa akan wannan cuta.” Wannan kudurin zai taimaka mana mu samu damar dakile yaduwar cutar a fadin kasar.