Afrika Ta Kudu Da India Na Fuskantar Karin Yaduwar COVID-19

Gwajin COVID-19 a Afrika ta kudu

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus ya linka zuwa 251,000 a Afrika ta kudu cikin makonni biyu, kasar India kuma ta ga adadi mafi yawa a ranar Asabar 11 ga watan Yuli yayin da gaba dayan wadanda suka kamu da cutar a kasar ya zarta 800,000. Hauhawar masu kamuwa da cutar da ake samu na kawo damuwa sosai akan bambancin da ake samu wajen jinyar cutar, yayin da masu hali ke sayen tarin kayayyakin asibiti su ajiye suna kuma amfani da asibitoci masu zaman kansu, talakawa kuma sun cika cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati.

Annoabr COVID-19 a India

Jami’ai sun ce adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya zarta kididdigar da jami’ar Johns Hopkins ta bada saboda karancin kayan gwaji, da rashin ingantaciyyar hanyar samun bayanai a wasu kasashen da kuma wasu matsalolin.

Wasu daga cikin kasashen da cutar ta shafa sosai na daga cikin kasashen duniya da aka fi samun wagegen gibin karfin fannin tattalin arziki a tsakanin al’umma. Afrika ta kuda na gaba-gaba a wannan kason, inda annobar ke nuna gibin da ake da shi a jinyar masu cutar.

A birnin Johannesburg, inda cutar ta fi kamari a Afrika ta kudu, na’urar shakar iska da ake matukar bukata, wadda ke taimaka wa masu coronavirus da ke fama da matsalar numfashi na da wahalar samu yayin da masana’antu masu zaman kansu da masu hali ke saye su, abinda Lynne Wilkinson kwararre a fannin lafiyar al’umma ya fada wa kamfanin dillancin labaran AP kenan.