Aiki Da Dokar Kare Kananan Yara Ya Zama Wajibi

Yara

Gwamnatin jihar Legas, a Najeriya, ta umarci hukumomi da sauran al’umar jihar dasu kasance masu aiki da dokokin dake bada kariya ga kananan yara masamman mata, da kuma sanya su makaranta, a watan Disamban da ta gabata ne Gwamnan jihar ya rattaba hannu akan wannan.

A wata sanarwa da babbar jami’a mai kula da hukumar dake bada kariya ga cin zarafin kananan yara a jihar ta Legas, Mrs. Titilola Adeniyi, ta bayar tace Gwamnatin jihar Legas, ta bada wannan umarni ne na tabbatar da amfani da wannan doka ganin yadda ake ci gaba da samun rahotani na cin zarafin kananan yara a jihar.

Mrs. Titilola Adeniyi, ta bayana cewa dokar na bada fiffiko ne wajan kare kananan yara tare da kuma tabbatar da cewa ana saka yara a makarantu domin samun kariya da kuma ilimi ingantatcen.

WEannan doka dai yana nufin Kenan iyaye da kuma wadanda ke rike da yaran dake hannun su dole ne su kasance suna bada kariya ga yara tare kuma da kuma kawar da cin zaerafin yara masamman a gidajen da ake amfani dasu a matsayin masu aikin gida.

Ms, Adenike Ese, wata jami’ar kungiyar sa kai mai tabbatar da lafiyar yara da kuma ‘yancin su a jihar ta Legas, tace kungiyarta ta gudanar da wani bincike inda aka gano cewa akalla rabin kananan yara dake birnin Legas, basu zuwa makaranta.

Your browser doesn’t support HTML5

Aiki Da Dokar Kare Kananan Yara Ya Zama Wajibi - 2'11"