Aisha Buhari Ta Marabci Sabuwar Jika

Aisha Buhari da sabuwar jikarta

Uwar gidan tsohon shugaban kasar Najeriya, Hajiya A’isha Buhari ta yi maraba da samun sabuwar jika, ta kuma dauki lokaci ta je domin kula da sabon jikanta da diyarta.

WASHINGTON, D. C. - Uwar gidan shugaban kasa mai ci, Oluremi Tinubu, da uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Hajia Nana Shettima, sun kai ziyar ga Aisha Buhari a bayan da ta koma gidanta.

Uwargidan Shugaban Kasar Najeriya Remi Tinubu

Oluremi Tinubu ta ce: “Abin farin ciki ne a gare ni da uwargidan mataimakin shugaban kasa, Hajiya Nana Shettima, da muka je gidan uwargidan tsohon shugaban kasar Najeriya, mai girma Dr. Aisha Buhari, domin taya ta murna bayan komawar ta gida daga ziyararta na ganin ‘yarta da sabon jikanta.”

"Allah ya albarkaci sabuwar jaririyar, iyayenta, da kakanni."

A shekarar 2022 ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi marhaban da jikan, wadda ta farko ne a gareshi.