Akalla Mutane 7 Sun Mutu A Hadarin Jirgin Ruwan Hungary

A yau juma’a masu ceto a birnin Budapest na kasar Hungary na cigaba da aikin tsamo wani jirgin ruwan yawon shakatawa daga kasan kogin Danube, yayin da suke neman mutane 21 da har yanzu ba’a gansu ba, bayan jirgin ruwan ya yi karo da wani makeken jirgin ruwa na wasu 'yan yawon shakatawa a shekaranjiya Laraba.

Sai dai ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 7, koda yake kuma an ceto wasu 7. Dukkan mutanen dake cikin jirgin, baya ga mutane biyu, sauran ‘yan kasar Koriya ta Kudu ne masu yawon shakatawa.

Gidan talabijin na kasar Hungary ya bada rahoton cewa dukkan mutane da aka ceto, an sallame su daga asibiti banda guda daya wanda ake jinyar sa saboda karyewar kashin hakarkari. 'Yan sandan kasar Hungary suna tsare da matukin jirgin ruwan mai suna Yuriy C.