Akwai Bukatar Dage Dokar Hawa Babur A Wasu Yankuna

Al’ummomin da suka koma yankunan su da aka kwato daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram, a Arewacin jihar Adamawa na kokawa game da rashin dage dokar hana amfani da babura da aka kafa, yau fiye da shekaru shida.

Wannan na zuwa ne lokacin da suke debo amfanin gona da sai an yi doguwar tafiya, batun da shugabanin al’ummar ke kira da a duba lamarin.

Yanzu haka dai wata matsalar dake addabar al’ummomin da suka koma yankunan su da aka kwato a hannun 'yan Boko Haram, na yankunan Michika da Madagali a Arewacin jihar Adamawan, shine na batun sufuri, sakamakon har yanzu hukumomin tsaro basu dage dokar hana amfani da Babura ba.

Yau fiye da shekaru shida ke nan da aka kafa wannan dokar, biyo bayan hare haren 'yan ta'adda.

Muhammad Hassan Oska, wani dan asalin yankin Michika ne, yace suna fuskantar matsaloli da dama.

Da yake karin haske Hon. Adamu Kamale dan majalisar wakilai dake wakiltar wadannan yankunan, ya bukaci hukumomin tsaro da su duba hali da kuma wahalar da ake fama da su, musamman wajen diban amfanin gona.

Ahmad Sajo, kwamishinan yada labarun jihar yace za’a duba batun, amma sai hukumomin tsaro sun amince.

Ko kafin zaben shekarar 2015, sai da gwamnan jihar Senata Muhammadu Bindow Jibrilla, ya shai da cewa idan aka zabe shi zai dage wannan dokar, kamar yadda lamarin yake a wasu jihohi.

Ga rahoton wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdul'aziz daga jihar Adamawa

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Dage Dokar Hawa Babur A Wasu Yankuna 3'20"