Akwai Mafita Game Da Batun 'Yan Shi'a Inji 'Yan Fafatuka

ABUJA: Mata 'yan shiya sun zanga zanga domin a sako shugabansu, Shaikh Ibrahim El-zakzaky

Kungiyoyin Kare hakkin bil’adama sun nuna damuwa game da rayukan da ke salwanta sanadiyar hargitsin dake wakana a tsakanin jami'an tsaron Najeriya, musamman sojoji da kuma kungiyar yan uwa Musulmi da akewa lakabi da “yan Shia.

Yau kusan kwanaki uku ke nan da samun wannan takaddamar sakamakon zanga zangar da yan kungiyar ta IMN, ta gudanar na neman gwamnatin kasar ta sako musu jagoransu Sheikh Ibrahim Yakub El Zakzaky.

Kungiyoyin Kare hakkin bani adama na ciki da wajen Najeriya sun nuna damuwarsu game da lamarin da suka ce kowanne bangare yana da hakin wanzar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda.

Yayinda kungiyar ke zargin hukumomi da kai masu hari baci bas ha, a wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce 'yan Shia sun far ma dakarunta da ke sanya ido a wuraren binciken ababen hawa, wanda ya zama dalilin daukar matakan tsaro.

Najeriya dai kasa ce dake bin tsarin da ya ba kowa “yancin addinin da ya ga dama ba tare da tsongoma ba.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz

Your browser doesn’t support HTML5

Tsokaci kan arangamar 'Yan Shi'a da sojojin Najeriya-1"56"