Akwai Sauran Aiki A Tattaunawar Cinikayyar Amurka Da China

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da ikirarin da China ta yi na cewa kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar rage haraji akan wasu kayayyaki da suka sanyawa juna a takaddamar cinikayyar da ke faruwa tsakanin kasashen biyu.

Ranar Juma’a Trump ya fadawa manema labarai a wajen fadar White House cewa, “sun so a rage haraji akan wasu kayayyakin (wato China kenan). “Amma ni ban amince akan wani abu ba.”

Wadannan kalaman na Trump sun nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba game da tattaunawar da bangarorin biyu ke yi don ganin sun kawo karshen mummunar takaddamar cinikayyar da ta shafi tattalin arzikin kasashen biyu.

Ranar Alhamis din da ta ne ma’aikatar cinikayyar kasar China ta ce kasashen biyu masu karfin tattalin arziki a duniya sun amince su rage haraji akan wasu kayayyaki da suka sanyawa juna.