Kungiyar tsagerun al-Shabab Ta Dauki Alhakin Kai Wani Hari Da Ya Hallaka Akalla Mutane Bakwai.

Jami'an tsaro a Somalia suke raga wani da ya jikkata a wani harin da al-shabab ta kai

Kungiyar tsagerun al-Shabab ta Somalia ta dauki alhakin kai wani babban hari da ya hallaka akalla mutane bakwai a babban birnin kasar a jiya Talata.

A cewar wasu da suka shedi al'amarin sun ce wata karamar motar bos ce, da aka dankara wa nakiyoyi ta abkawa helkwatan gundumar Wadajir na birnin Mogadishu dake yankin kudancin birnin da misalin karfe 12 da minti 40 na rana agogon kasar.

Wakilin sashen Somalia na Muryar Amurka Abdulkadir Mohamed Abdulle ya na wurin da al'amarin ya faru, kuma yace yaga gawarwaki guda bakwai.

Mutane da dama suka makale karkashin buraguzan ginin don haka ana sa ran adadin wadanda suka mutun zai karu inji wakilin na sashen Somalia.

Pashewar bam din ya auku ne kwanaki bakwai bayan kungiyar da al-Shabab ta kaiwa gidajen cin abinci guda biyu a Mogadishu hari da wata motar dake dauke da bam da kuma harbin bindiga. Wadannan hare haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane 29 ciki har da yan bindigan.