Al-Shabab Ta Kai Hari A Mugadishu Mutane 18 Ciki Harda Wasu Maharan Sun Halaka.

Wasu jama'a kenan a inda aka tayar da bam din

Daga Somalia kuma mun sami labarin cewa mayakan sakai na kungiyar al-shabab sun kai hari da bamabamai da bindigogi kan majalisar dokokin kasar, akalla mutane 18 sun halaka sakamkon farmakin, cikin matattun harda wasu daga cikin maharan.
Kakakin rundunar ‘Yansandan kasar Kasim Ahmed, ya gayawa Sashen Somalia na MA cewa jami’an tsaro 10 ‘yan kasar wadnada suke aiki da rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar hada kan kasshen Afirka da ake kira AMISOM suna daga cikin wadnada suka halaka a harin da aka kai kan ginin da aka yiwa tanadin tsaro sosai. Yace wasu jami’an tsaro 14 sun jikkata, da wakilan majalisa hudu.
Kakakin rundunar ‘Yansanda Ahmed Roble yace an kashe takwas daga cikin maharan.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai da wannan hari wanda ta kira “ragwanci”, kuma mummunar harin ta’addanci.Sanarwar da MHWA ta fitar tace Amurka tana ci gaba da bada cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Somalia da kawayenta na kasa da kasa wadanda suke goyon bayan kasar Somali a kokarinta na yaki da kungiyar al-shabab mai alaka da al-Qaida.