Al'umar Mozambique Na Fuskantar Barazanar Matsananciyar Yunwa

Wani mutum yana jira a raba a abinci a wani sansanin da aka ajiye 'yan gudun hijira bayan aukuwar guguwar Idai a yankin Dombe, na aksar Mozambique, 4 watan Afrilu, 2019.

Hukumar dai na so ne ta rika tallafawa mutum dubu 560 a kowanne wata, daga nan har zuwa cikin watan Oktoba, musamman ma a yankunan da guguwar ta yi barna.

Hakumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa, ‘yan kasar Mozambique miliyan 1.9 da mahaukaciyar guguwa ta daidaita rayuwarsu a farkon shekarar nan, na iya fuskantar matsalar karancin abinci, muddin kasashen duniya ba su kawo daukin gaggawa ba.

Daruruwa mutane ne dai suka mutu, sannan wasu dubbai suka rasa muhallansu bayan da guguwar Idai da ta Kenneth suka abkawa kasar ta Mozambique a watannin Maris da Afrilu.

Barnar da guguwar ta yi, sun lalata ababan more rayuwa da kuma amfanin gonakin al’umar kasar.

Kakakin hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duniya, Herve Verhoosel ya ce jama’a da dama na iya shiga kangin yunwa.

“Ana fargabar lokacin da za a shiga, zai zamanto mai matukar wahala, yayin da jama’ar da yawansu ya kusa miliyan biyu, aka yi hasashen za su tagayyara idan har ba a kai musu dauki ba.” Inji Verhoosel.

Hukumar dai na so ne ta rika tallafawa mutum dubu 560 a kowanne wata, daga nan har zuwa cikin watan Oktoba, musamman ma a yankunan da guguwar ta yi barna.