Algeriya Ta Tsa Keyar Wasu 'Yan Nijar Fiye da Dubu Zuwa Kasarsu

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijar Issoufou da Firayim Ministansa Birgi Rfiji

Kasar Algeriya na cikin kasashen da suka daukan hankalin 'yan Nijar 'yan cirani dake zuwa sana'ar bara inda akasarinsu mata da yara ne

Duk matakan da gwamnatin Algeriya ke dauka na takawa 'yan kasar Nijar birki basu daina zuwa kasar ba ta barauniyar hanya.

Karamin jakadan Nijar a Algeriya Alhaji Alatu Mugaskiya yace 'yan Nijar maza da mata da yara 119,000 hukumomin Algeriya suka tasa keyarsu zuwa kan iyaka da Nijar.A nan ne za'a tantancesu, a sanarda gwamnonin jihohinsu, su turo da motoci su kwashesu.

Shirin na gwamnatin Algeriya na tura keyar mutane zuwa kasashensu ya shafi 'yan wasu kasashen dake makwaftaka da Nijar kamar Mali wadanda su dubu hudu aka tura kasarsu.

Tun daga shekarar 2011 kawo yanzu daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a kokarin ketarewa zuwa Aljeriya ko Libiya.ko nahiyar Turai kamar yadda shugaban Nijar Issoufou Mahammadou ya fada. Ya kuma da kara cewa daga yanzu gwamnatinsa zata yi yaki da masu safarar mutane daga asarsa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Algeriya Ta Tsa Keyar Wasu 'Yan Nijar Fiye da Dubu Zuwa Kasarsu - 2' 59"